بسم الله الرحمن الرحيم
!!إنا لله وإنا إليه راجعون
ShekhKamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Zakzaky da mabiyansa sun yi tir da kona Alkur'ani a kasar Sweden sun masu kira da a gaggauta hukunta wanda sukai wannan mummuna aiki na cin zarafin addinin Allah.
Wannan labari mara daɗi na cin zarafin Alƙur'ani mai girma a ƙasar Sweden, ya raunata zukatan dukkanin musulmi da masu neman 'yanci na duniya. Tabbas kona Alƙur'ani mai tsarki ba wai cin fuska ne ga Musulunci da musulmi ba, cin fuska ne ma ga dukkanin addinan duniya da mabiyansu. Don haka, ya zama wajibi ga duk wani mai ƴanci da kada ya yi shiru akan wannan aiki.
Mun yi Allah wadai da wannan mummunan aiki da waɗanda suka aikata shi kuma muna kira da a gaggauta hukunta su.
Muna bayyana takaici da alhininmu na cin zarafin Alqur'ani da wani la’ananne ɗan ƙasar Sweden ya yi, inda ya ƙona littafin Allah mai tsarki.
Kamar yadda jagoranmu Shugabanmu Sayyid Ibraheem Yaqub Al-Zakzaky (H) ya faɗa cewa; wannan cin zarafi ne ba wai kawai ga Alqur'ani ba ko ga musulmi ba a’a cin zarafi ne ga dukkan litattafai da dukkan addinai.
Dan haka muna masu bin sahun jagoranmu wajan nuna takaicinmu da yin tir gami da Allah wadai da wannan ta’asa. Allah Ka ƙara daɗin tsinuwa ga wannan munkiri da ƙasar Sweden, ka nuna masu isarka da ikonka kamar yadda ka faɗa a cikin littafin nan naka mai tsarki da aka wulakanta, cewa:
إِنَّا نَحْنُ نَزَّلْنَا الذِّكْرَ وَإِنَّا لَهُ لَحَافِظُونَ.
@SyykFacebookPage
DeathToSweden
01/07/2023